XtGem Forum catalog
Sulaiman20Ibn20Hujjah 2
Barka20Da20Zuwa
Shafi20Mai20Albarka



¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶

Zaka iya kiran wayata tanan
HomeBlogAbout MeBayani Akan AZUMIAikin Hajji da UmaraMa anar Shi aAbin da Aka HanaSamun FalalaKasuwanci Mai RibaMahimmancin Addu o iBayanin ZakkaSALLAMATA A MUSULUNCITSARKITAUHEEDI DA AQIDAAYYUKAN ZUCIYAMAHIMMANCIN DA AWATAMBAYA DA AMSASheikh jafar mahmud AdamWadansu websides


SHIGA NAN DOMIN SAMUN KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH


Sheik Lawan Abubakar Gadon Kaya tafseer2017



02/05/24
FB Pantami


Ibn20Hujjah
Source: Google news
0Mozilla/5.0




SULAIMAN Ibn Hujjah

* No categories

Online: Guests: 1


Sulaiman20 FaceBook


**KASUWANCI MAI RIBAR GASKE**

Lallai Allah (S. W .T) Ya fifita mutum a kan sauran halittu, sa'an nan ya kebe mutum da ni'im ta shi da yin magana, ya sanya na'urarsa ita ce harshe, ni'ima ce wadda za a iya amfani da ita wajen aikata alheri ko sharri.
Duk wanda yayi amfani da ita wajen alheri, lallai ya rabauta a duniya, da masaukai madaukaka a cikin aljanna.
Duk kuma wanda yayi amfani da ita ta akasin haka (wata ta sharri) to lallai halaka ta riske shi duniya da lahira.
Mafificin lokacin da mutum zai rabauta da shi bayan karatun Alkur'ani shine zikri (ambaton Allah).

**FALALAR ZIKRI**
Ya tabbata a cikin hadisai masu yawa, daga cikin fadin Manzon Allah (s a w): "Shin ba na baku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen sarkin da yake mallakar ku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku daga ciyar da zinariya da azurfa, kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku rika dukan wuyansu, suna dukan wuyanku? Suka ce kaba mu labari. sai yace: Ambaton Allah Madaukaki.
"Kuma Manzon Allah, (s a w) yace: "Misalin wanda yake ambaton ubangijinsa da wanda ba ya ambaton ubangijinsa, kamar misalin rayayye da matacce ne".

"Kuma yace" Allah, madaukaki yana cewa: Ni ina nan inda bawana yake zato na, kuma ina tare da shi idan ya ambace ni.
Idan ya ambace ni a cikin ransa zan ambace shi a cikin rai na, idan ya ambace na a cikin jama'a zan ambace shi a cikin jama'ar da ta fi su alheri, in ya kusance ni da kamar kamu daya zan kusance shi tsawon gaba guda, in ya zo min yana tafiya zan zo masa ina sassarfa".
Kuma Manzon Allah (s a w) yace : masu kadaita sun yi gaba, aka tambaye shi su waye masu kadaita? sai yace masu ambaton Allah da yawa,.
Kuma Manzon Allah (s a w) ya kasance a wani lokaci mai wasiyya ga wani sahabinsa; yace "kar harshenka ya gushe yana danye saboda ambaton Allah".

**SAKAMAKON LADA**
Ana ninninka sakamakon kyawawan ayyuka kamar yadda ake ninninka sakamakon karanta Alkur'ani saboda gwargwadon abin da yake cikin zuciya na imani da tsarkake niyya da kuma son Allah na hakika da abin da yayi kama da haka.
* Ana ninninka sakamakon ayyukan na kwarai saboda gwargwadon yawan tunanin zuciya da ambaton Allah da kuma mai da hankali akan haka.
Ambato da harshe kawai babu tunanin zuciya akan haka baya isa. idan aka samu wadannan to Allah zai kankare kurakuran mutum duka kuma ya bashi sakamako na lada cikakke. wanda ya tauye shi ma zai samu gwargwadonsa.

SHIGA NAN DOMIN SAMUN KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH ASAUKAKE
**FAIDOJIN ZIKIRI**
Zikiri ya na koran shaidan, yana takura shi, yana wulakanta shi kuma yana kaskanta shi kuma Allah (mai rahama) yana yarda da mai yinsa.
* Zikiri yana gadar da soyayyar Allah da kuma kusanci zuwa gare shi, da kuma samun kwarjini daga gare shi da kuma mayar da al'amari da komawa zuwa gare shi, da damuwa, kuma ya sanya farin ciki da gadar da rayuwa maikyau, karfi da kuma tsarki.
* A cikin zuciya akwai gurbin talauci babu abin da ke toshe wadannan abubuwa sai ambaton Allah (s w t), kamar yadda kuma akwai kaikashewa a cikinta wadda babu abin da ke tausasa shi sai ambaton Allah.
* Zikiri waraka ne ga zuciya kuma magani ne gare ta, kuma dalili ne na samun karfi, da jin dadi wanda babu kamar sa, kuma gafala daga barin ambaton Allah ciwo ne ga zuciya.
* Karancin ambaton Allah alamar munafunci ne, ya waita shi alamar karfin imani ne da kuma gaskiyar soyayya ga Allah (s w t) domin duk mai son wani abu zai yawaita ambatonsa.

* Kuma bawa idan ya tuna da Allah a lokacin da yake cikin yalwa, Allah zai tuna shi a lokacin da yake cikin tsanani, musamman a halin mutuwa da magaginta.
* Zikiri dalili ne na samun tsira daga azabar Allah (s w t) da kuma samun natsuwa, lullubewar rahama da kuma samun neman gafara da mala'iku.
* Harshe na samun kariya daga wasanni, da cin naman mutane da annamimanci, karya da sauransu na abubuwan ki da kuma na haramun.
* Zikiri shi ne mafi sauki daga cikin ibadoji, kuma shi ne mafi girma da falala, kuma da shine ake abun shukar gidan aljanna.
* Zikiri na gadar da kwar-jini da jin dadi kuma annuri ga fuska; haske ne a nan duniya ,da kuma a kabari da ranar kiyama.
* Zikiri na haifar da samuwar yabo daga Allah da kuma mala'ikunsa ga mai yinsa. Allah (s w t) yana alfahari da masu ambatonsa da mala'iku.

* Mafifici daga masu bauta sune wadanda suka fi ambaton Allah (s w t) da yawa, kuma wadanda suka fi falala daga masu yawaita azumi su ne wadanda suke ambaton Allah a lokacin azuminsu.
* Zikiri na sauwake wahala, kuma ya na sauwake tsanani, yana kuma saukaka kunci, yana jawo arziki kuma yana karfafa jiki.
Shaihin malami nan Ibn Taimiyya yace: "Zikiri ga zuciya kamar ruwa ne ga kifi, kaga yaya zai kasance rayuwar kifi in har ya rabu da ruwa?"
^^^TO KAGA WANNAN SHINE KASUWANCI MAFI RIBA A RAWUWA^^^

Sulaiman20Ibn20Hujjah-1 4